Amsar wannan tambayar yana da rikitarwa. Mutane da yawa baza su iya gaya ma jami’an lafiya ba musamman a kasashe da ba’a sa doka game da madugu, luwadi, masu canza jinsi da mata-maza ko kuma a kasashen da babu sirri tsakanin likita da mara lafiya.
Idan muna iya amincewa da jami’an lafiyan mu, za su iya kula da mu da kyau. Idan ka yi magana da su game da jinsi, da kuma irin jima'i da kake yi zasu iya sanin gwaje-gwajen da kake bukata domin lafiyan ka.
Ka tuna cewa ka cancanci samun kwararen likita da za ka iya Magana da shi ba tare da kunya ba. Idan likita ya yi ƙoƙarin gaya maka cewa tsarin jima'in ka ba daidai ba ne, ka gaya masa cewa kana son ku yi magana game da magani kawai a lokacin ziyarar ka.
Domin Karin bayyani game da kanjamau, a kalla wanan bidiyo. (Wurin dubawa da turanci)